Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojojin Najeriya sun cimma wa'adin murkushe Boko Haram

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa rundunar sojin kasar ta cimma wa’adin da aka ba ta na murkushe kungiyar Boko Haram a cikin wannan watan na Disamba.

Dakarun Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Dakarun Najeriya da ke yaki da Boko Haram AFP PHOTO/HO/NIGERIAN ARMY
Talla

Ministan yada labarai da raya al’adun kasar ne Lai Mohammed ya sanar da haka a lokacin da ya gana da shugabannin kafafan yada labarai a jihar Legas da ke kudancin kasar.

Ministan ya ce, an samu gagarumar nasara a yaki da kungiyar kuma a cewarsa, ya fadi haka ne saboda kwanan-nan ya jagoranci tawagar ‘yan jarida na gida da kasahen waje zuwa garuruwan Maiduguri da Konduga da Kaoure da Bama.

Ministan ya ce, yanzu haka hanyar da ke tsakanin Maiduguri da Bama mai nisan kilomita fiye da 70 da kuma hanyar Banki da ake bi zuwa Kamaru da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na hannun dakarun Najeriya.

To sai ministan ya koka da hare haren kunar bakin wake da ake ci gaba da kaiwa a kasar, inda ya ce wannan matsalar ta’addanci ce da ake fama da ita a duniya baki daya.

Jim kadan da kama aiki a matsayin shugaban kasa, Buhari ya bukaci sojojin Najeriya da su murkushe mayakan Boko Haram nan da ranar 31 ga watan Disamba na bana.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.