Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC ta kama tsohon gwamnan Kaduna, Jafaru Isa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin jagororin jam’iyyar APC mai mulkin kasar, Jafaru Isa bisa zargin sa da hannu a badakalar karkatar da alakar Dala biliyan 2.1 da aka ware domin siyan makaman yaki da Boko Haram.

RFI / Pierre Moussart
Talla

Tun lokacin da hukumar ta fara bincike kan lamarin, a karon farko kenan da ta kama wani kusa a jam’iyyar APC.

Alhaji Jafaru wanda ya yi gwamnan jihar Kaduna a lokacin mulkin soja, na da kyakkyawar alaka da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Kanar Sambo Dasuki.

Hukuamr ta cafke shi ne a gidansa da ke titin Ajayi Crowther na unguwar Asokoro a birnin Abuja bayan ta kai samame da misalin karfe 9 na daren jiya laraba.

Bincike ya nuna cewa Alhaji Jafaru ya karbi Naira miliyan 100 daga hannun Sambo Dasuki.

Tuni dai shugaban EFCC Ibrahim Magu ya ce babu sani babu sabo kan ayyukan da hukumar ke gudanarwa dangane da shirin kwato makudan kudaden talakawan da aka yi rub da ciki da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.