Isa ga babban shafi
Najeriya

Akalla ‘an fashin shanu 39 suka tuba tare da mika makamansu...

Akalla ‘an fashin shanu da wasu ‘yan fashi da makami 39 ne suka mika makamansu ga rundunar ‘yan sandan jihar Kano, don cin moriyar shirin yafiyar nan da gwamnatin jihar tayi musu tayi.

Adelere Shinaba, Komishinan yan Sandan jahar Kano.
Adelere Shinaba, Komishinan yan Sandan jahar Kano. AFP PHOTO/AMINU ABUBAKAR
Talla

Gwamnan jihar dr Abdullahi Umar Ganduje tare da Kwamishinan ‘yan sandan jihar MUHAMMAD Musa Katsina ne suka karbi makaman a cen dajin Gommo na Karamar hukumar Sumaila.

Acewar gwamnatin Kanon zata kula da rayuwar su ta hanyar basu aiyukan yi, tare da tarbiyyar komawa mutane na gari.

Abaya dai jihar tayi fama da barayin shanu, da ‘yan fashi da makami dake cin Karen sub a bau babbaka a dazukan jihar.

Koda a yan makoninnan saida rundunar ‘yan sandan jihar ta cafke fiye da ‘yan fashi dari, tare da kwato shanu da rakuma
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.