Isa ga babban shafi
Najeriya

Saraki ba zai yi murabus ba- Ndume

Jagoran majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume ya bayyana cewa, shugaban majalisar Bukola Saraki ba zai yi murabus ba daga mukaminsa har sai kotun ladabtar da ma’aikata ta kasar ta same shi da aikata laifin da ake zarginsa akai.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki. ynaija.com
Talla

Ndume ya shaida wa manema labarai haka ne a fadar shugaban kasar  da ke birnin Abuja bayan ya kammala ganawa da mukaddashin shugaban kasar, Yemi Osinbajo a jiya Talata.

Har ila yau, Ndume wanda ya samu rakiyar Dino Melaye da Abdullahi Adamu ya bayyana kiraye-kirayen da ake yi na cewa Saraki ya sauka daga kujerarsa a matsayin garaje, sannan ya ce, kuskure ne a caccake sa kafin kotun ta same shi da laifi

Saraki dai na fuskantar tuhuma ne sakamakon zargin da ake yi masa kan bayar da bayanan karya dangane da kadarorin da ya mallaka a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kwara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.