Gwamnatin Borno za ta bude manyan hanyoyi
Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin tarayyar Najeriya ta ce, ta na shirin sake bude manyan hanyoyin da suka hada birnin Maiduguri da sauran sassan jihar.
Wallafawa ranar:
Gwamnan jihar, Kashim Shettima ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da 'yan kasuwa da ke gudanar da harkokinsu a kasuwar Monday Market da ke Maiduguri.
Gwamnan ya ce, ya sanar da daukan matakin ne domin farfado da tattalin arzikin jihar wanda ya gamu da koma baya sakamakon hare-haren kungiyar Bokom Haram.
Tuni dai gwamnatin Shettima ta gina shagunan hada hadar kasuwanci a sassan daban daban na babban birnin jihar domin karfafa gwiwar ‘yan kasuwa.
Gwamnan dai ya yi amanna cewa, nan ba da jimawa ba za a kawo karshen kungiyar Boko Haram da ta dade ta na ta’asa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu