Isa ga babban shafi
Nigeria

Sojan Nigeria sun bude Manyan hanyoyin tafiya Maiduguri.

Rundunar Sojan Nigeria ta bude wasu manyan hanyoyi da ba'a bi saboda matakan tsaro tsakanin birnin  Maiduguri jihar Borno zuwa sassan jihar,  bayan rufe wadannan hanyoyi na tsawon shekaru uku sakamakon hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa jama'a. 

Babban Hafsan sojan Nigeria Tukur Buratai
Babban Hafsan sojan Nigeria Tukur Buratai AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Babban Hafsan sojan kasa na Nigeria Laftanar Janar Tukur Buratai ya sanar da haka, a garin Damboa, a yayinda yake kaddamar da wasu Babura da sojan zasu rika amfani dasu domin farautar ‘yan kungiyar Boko Haram.

A cewar Laftanar Janar Tukur Buratai sojan za su ci gaba da kokarin kare lafiyar jama'a da dukiyoyin su, inda yace babbar hanya tsakanin Maiduguri zuwa garin Biu an bude ta.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.