Isa ga babban shafi
Najeriya

Wani abu da ya fashe ya hallaka mutane 2 a Calabar

Hukumomi a Jihar Cross River dake Najeriya sun musanta rahotanni dake cewa bam ya tashi a reshen harabar babban bankin kasar dake birnin Calabar inda mutane 21 suka jikkata

Birnin Calabar na jahar Cross River a Najeriya
Birnin Calabar na jahar Cross River a Najeriya Nigeriamissionhome.com
Talla

Mutane 2 yanzu haka shedun gani da ido ke cewa sun mutu sakamakon fashewar, amman kuma mataimakin Sufetan ‘Yan sanda Jihar Baba Abisa Bolanta ya ce babu shakka abu ya fashe amma babu tabbacin cewar bam ne, inda yace ana kan binciken gano asalin fashewar.

A Najeriya anyi ta fama da hare-haren bama bamai a yankin arewa maso gabashin kasar, inda dubban mutane suka rasa rayukansu sakamakon ayyukan kungiyar nan ta Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.