Isa ga babban shafi
Najeriya

Jihar Ribas ta daura alhakin rikicin zabe kan Sojoji

Gwamnatin jihar Ribas dake Tarayyar Najeriya ta zargi Rundunar sojin Najeriya da haifar da rudani da ya kai ga samun tashin hankali a wasu mazabun Kanana hukumomin jihar lokacin zaben cike gurbi ‘yan majalisun da aka sauke a karshan makon daya gabata.

Zaben Najeriya
Zaben Najeriya Photo: Reuters/Akintunde Akinleye
Talla

Tahse-tahse hankulan lokaci da harbe harbe ya kai ga rasa rayukan mutane 4, a karamar hukumar Bonny da Elemi dake Jihar ta Ribas.

Toh sai dai a zantawarsa RFI hausa, Sakataren Gwamnatin Jihar Kenneth Kobani, ya daura alhakin tashin hankali kan jami’an Sojin Najeriya.

A cewar Mista Kenneth Jami’an Sojin sunyi kokarin yin katsalanda kan harkokin zabe, ta hanyar gudanar da abubuwa da suka sabawa doka, tare da tilasatawa jama’a zaben wadanda ba suyi niya ba, bayan gabatar da takardun zaben Boge.

Jami’an sun kuma kokarin kawo wasu kayayyakin zabe da hukumar INEC bata san dasu ba cikin hada sakamakon Boge, kokarinsu shine a zabe APC, a cewar Kenneth.

Sakataren ya kuma bayyana yadda aka kame mutane da dama da basu da laifi a wannan rana.

Kan wannan batu mukayi kokarin ji daga bakin Rudnunar Sojin Najeriya, to sai dai ta ce ba zata ce Uffan ba, saboda aikinsu shine samar da tsaro kuma hakan akayi a wannan ranar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.