Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar musulmi ta kai Buhari ICC saboda rikicin Shi'a

Wata Kungiyar kare hakkin musulmi da ke da ofishinta a Birtaniya ta gabatar da kokenta ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, inda ta ke zargin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hafsan sojin kasar Tukur Buratai da gwamnan Kaduna El-rufa'i da yi wa ‘yan Shia kisan kiyashi a garin Zaria.

Jagoran mabiya  Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Jagoran mabiya Shi'a a Najeriya El-Zakzaky
Talla

Kungiyar ta kuma bukaci Kotun da ta binciki sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu da kuma sarkin Zaria, Shehu Idris sakamakon wannan rikici tsakanin sojojin Najeriya da mabiya Shi’a a watan Disamban bara.

Wannan na zuwa ne a wani lokaci da ayarin wasu Lauyoyi su ka gana da manema Labarai a jihar Kaduna domin neman a sako jagoran Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da ake tsare da shi.

Suhaila Ibrahim El-Zakzaky na daga cikin ‘ya’yan malamin da ke raye kuma ta halarci wannan taron na manema Labaran inda ta ce, ba su da masaniya game da inda aka boye mahaifisnu, sannan ta koka akan halin da suka tsinci kan su a ciki.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.