Isa ga babban shafi
Najeriya

Satar Dala biliyan 15 ta jefa Najeriya cikin kunci

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, asarar da kasar ta yi ta Dalar Amurka biliyan 15 da aka ware domin siyan makaman inganta tsaro, ta yi lahani ga tattalin arzikin kasar.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo tvcontinental.tv
Talla

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana haka a wani taron biki da ya halarta a jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo.

Ana zargin tsoffin jami'an gwamnatin da ta shude ta Goodluck Jonathan da wawure makuden kudaden da yawansu ya kai kimanin rabin abinda ke cikin asusun waje na Najeriya.

Osinbajo ya ce, wannan gwamnatin ba za ta kyale duk wani jami’in da aka samu da hannu a cin hanci da rashawa ba.

Sannan ya ce, duk wanda aka kama, sai ya amayar da abinda ya ci kuma ya fuskanci hukunci kamar yadda shari’a ta tanada.

A bangare guda, mataimakin shugaban ya ce, gwamnatin Najeriya za ta samar da Megawatt na wuta guda dubu 7 cikin watanni 18 masu zuwa, sai dai ya koka da matsalar fasa bututun mai da ake fama da ita a kasar, yayin da shugaba Buhari ya umarci jami'an soji da su sa ido kan bututun man .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.