Isa ga babban shafi
Najeriya-kamaru

Najeriya da Kamaru za su yi musayar 'yan Boko Haram

Shugabannin Najeriya da Kamaru sun amince su yi musayar wadanda ake zargi 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne don yi mu su shari’a a kasashensu.

Shugaba Paul Biya na kamaru da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya
Shugaba Paul Biya na kamaru da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya STRINGER / AFP
Talla

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Kamaru Paul Biya sun bayyana haka ne bayan kammala ziyarar kwanaki biyu da Paul Biya ya kai Najeriya.

Kasashen biyu sun jaddawa aniyarsu ta ci gaba da yaki domin kawo karshen kungiyar Boko Haram da ke tayar da kayar baya a yankin arewa maso gabashin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

Shugaba Buhari ya mika godiyarsa ga kasashen G7 masu karfin tattalin arziki a duniya kan irin gudun mawar da suke bayar wa wajen kakkabe mayakan Boko Haram da suka kashe mutane da dama tare da raba wasu da gidajensu.

Wakilinmu daga birnin Abuja, ya aiko mana da rahoto kan ganawar Buhari da Paul Biya

01:38

Ganawar Buhari da Paul Biya

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.