Isa ga babban shafi
Najeriya

Za a daure malaman da ke lalata dalibai a Jami'oin Najeriya

Majalisar dattawan Najeriya ta yi karatun farko kan wani kudurin doka da ya bukaci daurin shekaru biyar ga duk malamin jami’ar da aka samu da yin lalata da daliba.

Mambobin majalisar dattawan Najeriya
Mambobin majalisar dattawan Najeriya 247nigerianewsupdate.co
Talla

Kudirin dokar wanda Sanata Ovie Omo-Agege ya gabatar kuma ya samu amincewar sanatoci guda 46, ya bukaci a haramta duk wata hulda da za ta kai ga yin lalata tsakanin malamai da dalibai a makarantun gaba da sakandare na Najeriya.

Sanata Omo-Agege ya ce, ya zama dole a tsaftace makarantun ta hanyar kawar da  malaman da ke lalata da dalibai mata.

Sanatan wanda ya fito daga jihar Delta, ya kara da cewa, da zaran an amince da kudirin dokar , to hakan zai bada damar daure wanda aka samu da laifi a gidan yari har na tsawon shekaru biyar ba tare da biyan tara ba.

Ana dai yawan kokawa kan yadda malaman makarantun gaba da sakandare ke cin zarafin dalibai mata ta hanyar lalata da su domin samun maki a jarabawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.