Isa ga babban shafi
CAF

CAF ta ci tarar Najeriya kan cunkoso a Kaduna

Hukumar kwallon kafa a Afrika CAF ta ci tarar Najeriya kudi dala dubu biyar kan laifin cunkuso da rashin wadaccen tsaro a wasanta da Masar a filin wasan Ahmadu Bello a Kaduna arewacin kasar.

Kimanin Mutane 40,000 suka kalli wasan Najeriya da Masar a Kaduna
Kimanin Mutane 40,000 suka kalli wasan Najeriya da Masar a Kaduna AFP via thenational
Talla

An buga wasan ne dai a ranar 29 ga Maris kuma sama da ‘yan kallo dubu Arba’in suka kutsa domin kallon wasan a filin na Kaduna mai daukar ‘yan kallo dubu sha biyar.

Gwamnatin Kaduna dai ta bude kofa ne ga ‘Yan kallo domin shiga kallon wasan kyauta.

Sai dai an tashi wasan ne ci 1 da 1, kafin Masar ta fitar da Najeriya a Alexandria a wasannin neman shiga gasar cin kofin Afrika da za a gudanar a Gabon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.