Amnesty ta bukaci a rufe barikin soji na Giwa
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnatin Najeriya data gaggauta sakin wasu mutane 1,200 da ake tsare da su a barikin soji na Giwa dake birnin Maiduguri na jahar Borno sannan ta rufe barikin baki daya.
Wallafawa ranar:
Amnesty ta yi kiran ne bayan gano cewar mutane 150 ne suka mutu ciki harda kananan yara 11 da jarirai sakamakon matsaloli da suka kunshi yunwa da kishirwa da kuma cututtuka.
Amnesty ta ce akalla mutane 150 da suka hada da kananan yara ne suka mutu a shekara 2016, a barikin sojin na Giwa.
A rahoton da kungiyar ta fitar yau Laraba, kungiyar ta yi zargin cewa ana tsare da mutanen ne a cikin wani mummunan hali da ya keta hakkin bil’adama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu