Buhari ya jadada bukatar murkushe tsagerun Niger Delta
Shugaban kasar Najeriya Muhammdu Buhari, ya bada umarni karfafa matakan tsaro a yankin Niger Delta dake kudancin kasar, yayin da ake cigaba da samun rahotanni hari kan bututun mai dake barazana ga tattalin arzikin kasar.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa daga ofishin shugabar kasar, ta umarci jami’an tsaron kasar su murkushe tsgerun dake haifar da nakasu ga cigaban kasar, ta hanyar fasa bututun mai.
Sai dai a cewar Philip Hammond ministan kasahen wajen Britaniya, daukan matakan soji ba zai shawon kan matsalar hari kan bututun mai a Najeriya ba, saboda talauci na daga cikin musabbin dake sanya mazauna yankin ta’addi ga bututun man.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu