Isa ga babban shafi
Najeriya

Farashin mai na dab da saukowa a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bai wa al’ummar kasar tabbacin cewa, nan ba da jimawa ba farashin lita guda na man fetir zai sauko daga Naira 145.

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo
Talla

Mataimakin shugaban kasar ne, Yemi Osinbajo ya tabbatar da haka a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga dimbin mutanen da suka taru a dandalin Tafawa Balewa da ke jihar Legas a jiya Litinin.

Mr. Osinbajo ya ziyarci jihar ce domin wakiltan shugaba Muhammadu Buhari wajen kaddamar da wasu ayyukan gwamnati.

Osinbajo ya ce, matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na bude kofofi ga 'yan kasuwa zai bai wa duk wani dan kasar damar shigo da mai matukar ya cika sharuddan da ake bukata, abinda zai haifar da faduwar farashin daga Naira 145 saboda yawaitan 'yan kasuwar kamar yadda mataimakin ya bayyana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.