Buhari zai je London dan neman magani
Yau litinin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai fara hutun kwanaki 10 wadda za ta kai shi birnin London dan kula da lafiyarsa.
Wallafawa ranar:
Femi Adeshina mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai yace tafiyar ta biyo bayan shawarwarin likitoci don samun kula na musamman daga kwararru saboda ciwon kunnen dake damun shugaban.
A baya an yi ta yayata labarin cewar Shugaba Buhari yana fama da jinya daya daga cikin dalilan da suka hana shi ziyara a Ogoniland a Niger Delta mai fama da matsalar barayin mai, sai dai kuma fadar shugaban ta musanta hakan a wannan lokacin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu