An yi jana'izar Amodu Shuaibu
Al’umma a Najeriya na ci gaba da nuna alhini dangane da mutuwar tsohon kocin tawagar kwallon kafa Amodu Shuaibu wanda ya mutu ranar juma'a yana da shekaru 58 a duniya.
Wallafawa ranar:
Tuni aka binne Amadou Shuaibu kamar yadda sharuddan musulunci suka gindaya, an kuma binne marigayin ne a mahaifarsa da ke Okpella na karamar hukumar Etsako a jahar Edo.
Shugaban kasar Muhammadu Buhari na daga cikin wadanda suka nuna kaduwa da mutuwar tsohon kocin ganin hakan ya faru ne kwanaki kadan da mutuwar Stephen Keshi wanda shima ya taba horas da 'yan wasan Super Eagles na kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu