Boko Haram ta sace mata a Borno
Rahotanni daga Najeriya sun ce, mayakan kungiyar Boko Haram sun kai sabon hari a wani kauye da ke kusa da garin Chibok na jihar Barno inda suka sace mata guda 3.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewa, kungiyar ta kai harin ne a kauyen Kautuva a jiya da asuba, inda ta kona gidaje tare da harbe wasu mazauna garin, kamar yadda wadanda suka tsallake rijiya da baya da kuma 'yan kato da gora suka sheda.
Wani mazaunin garin Ali Pagu ya ce, da kyar suka sha kafin daga bisani su tsere zuwa garin Chibok domin samun mafaka.
A watan Aprilun shekara ta 2014 ne, kungiyar ta Boko Haram ta sace 'yan matan sakandaren garin Chibok fiye da 200, al'amarin da ya janyo cecekuce a duk fadin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu