Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya na bincike kan zargin 'ya'yanta da lalata

Majalisar wakilan Najeriya ta fara gudanar da bincike kan wata wasika da ta samu, inda Amurka ta zargi mambobinta da yunkurin yin fyade da kuma neman karuwai a lokacin da suka ziyarci Cleveland na Amurka don halartar wani taro.

Majalisar wakilan Najeriya na binciken mambobinta kan zargin da ake yi musu na yunkurin yin lalata da karuwai a Amurka
Majalisar wakilan Najeriya na binciken mambobinta kan zargin da ake yi musu na yunkurin yin lalata da karuwai a Amurka AFP
Talla

Shugaban kwamitin yada labaran majalisar Hon. Abdurrazaq Namdaz ya shaida wa RFI hausa cewa, sun samu wasikar daga jakadan Amurka a Najeriya, James Entwistle a ranar 9 ga wannan wata na Yuni kuma tuni suka fara aiki akan wasikar don tabbatar da gaskiyar lamarin.

Hon. Namdaz ya ce, za su sanar da duniya da zaran sun kammala binciken.

 

00:46

Hon. Abdurrazaq Namdaz kan zargin 'yan majalisa da kokarin lalata

Wasikar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin da suka hada da Samuel Ikon na jam’iyar PDP daga jihar Akwa Ibom da Mohammed Garba Gololo na jam’iyyar APC daga jihar Bauchi, sai kuma kuma Mark Gbillah na APC daga jihar Benue.

Wasikar ta zargi Gololo da rungumar wata ma’aikaciyar Otel, sannan kuma ya nemi yin lalata da ita.

Mr. Ikon da Gbillah kuwa, sun bukaci masu kula da wuraren ajiye motoci da su nemo masu karuwai kamar yadda wasikar ta bayyana.

Rahotanni sun ce, tuni Amurka ta soke Bisar tafiye tafiye na wadannan 'yan majalisa da ake zargi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.