Isa ga babban shafi
Najeriya

Rikicin PDP ya sake rincabewa

A Najeriya yanzu haka magoya bayan jam’iyyar PDP na can a birinn Port Hacourt domin sabunta kwamitin gudanarwar jam’iyyar, to sai dai ana gudanar da taron ne a daidai lokacin da wani bangare na jam’iyyar ke nuna adawa da hakan.

Tutar Babbar  jama'iyar awada ta PDP a Najeriya
Tutar Babbar jama'iyar awada ta PDP a Najeriya
Talla

Ana dai takaddama ne tsakanin kwamitin gudanarwar jam’iyyar a karkashin jagorancin Ahmed Makarfi da kuma bangaren Ali Modu Sherif.

Tsohon gwmanan jihar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa da ke goyon bayan taron na birnin Port Hacourt, ya ce lura da irin mutanen da ke shirin halartar wannan taro, alama ce da ke tabbatar da cewa ba wata barakar a jam’iyyarsu.

To sai dai Ali Modu Sheriff da kuma mukarrabansa sun bayyana taron na yau a matsayin wanda ya sabawa doka, kamar dai yadda mai Magana da yawunsu Inuwa Buwala ke cewa.

Tuni Babbar Kotun Abuja ta bukaci a hanna gudanar da wannan taro data haramta.

Tun bayan da PDP ta rasa mulkin Najeriya a shekarar 2015 ne jam'iyyar ke fuskantar rikici na cikin gida, lamarin da ke kara Rincabewa a Kullum.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.