Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

'Yan gudun hijira sun yi zanga-zangar yunwa a Maiduguri

Daruruwan ‘yan gudun hijira da ke cikin sansanoni da aka kafa a garin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya ne suka gudanar da zanga-zanga a wannan alhamis inda suke nuna rashin jin dadinsu a game da rashin abinci da ruwan sha a inda aka tsugunar da su.

'Yan gudun hijiran Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya
'Yan gudun hijiran Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya REUTERS/Stringer
Talla

Masu zanga-zangar dai sun toshe babbar hanyar da ta tashi daga Kano zuwa Maiduguri na tsawon lokaci, yayin da jami’an tsaro ke gefe domin tabbatar da doka da oda.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar UNICEF ta ce akalla mutane 49,000 ake sa ran za su mutu a Arewa maso Gabashin Najeriya bana saboda karancin abinci mai gina jiki.

Sai dai jami’an hukumar NEMA sun ce suna da isasshen abincin kula da 'yan gudun hijirar.
 

00:55

'Yan Gudun Hijira na kukan yunwa

Bilyaminu Yusuf

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.