Buhari ya jinjina wa shugaban Facebook
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa shugaban kamfanin sadarwa na facebook, Mark Zuckerberg game da kokarinsa na kara wayar da kan matasan kasar a fannin fasahar sadarwa.
Wallafawa ranar:
Shugaban ya yaba wa Zuckerberg ne bayan ya gana da shi a fadarsa da ke babban birnin Abuja a yau Jumma’a.
Saukin kan Zuckerberg wanda shi ne na biyar wajen arziki a duniya ya kayatar da Buhari, musamman yadda matashin ya cakudu da talakawan Najeriya a ziyar da ya kai.
A cewar shugaba Buhari, ba su saba ganin fitattun mutane kamar Zuckerberg na sassarfa a kan tituna ba har ta gai ga yin zufa.
A na shi bangaren, Mr. Zuckerberg mai shekaru 32 ya yaba da irin fasahar da matasan Najeriya ke da ita musamman a bangaren sarrafa kwamfuta kamar yadda ya gani a garin Yaba da ke jihar Legas a kudancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu