Isa ga babban shafi
Najeriya

Hukumar SEMA ta musanta samun asarar rai a Kaduna sakamakon motsawar kasa

Hukumar bada agajin gaggawa SEMA da ke jihar Kaduna a Najeriya, ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon motsawar da kasa ta yi a kauyen Kwoi a karamar Hukumar Jaba a Kudancin jihar.

Malam Nasir El Rufa'i Gwamnan jihar Kaduna
Malam Nasir El Rufa'i Gwamnan jihar Kaduna via El rufa'is facebook page
Talla

Sakataren Hukumar ta SEMA Ezekiel Baba-Karik ya kuma musanta rahotannin da ke cewa, an kuma samun motsawar kasar a Kauyukan Nok da Sambang Dagi, da ke karamar hukumar ta Jaba kamar yadda wasu ke yadawa.

Baba-Karik ya ce tuni aka aike da tawagar masu bincike yankin domin gano musabbabin motsawar kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.