Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne kan shirin gwamnatin Najeriya na bunkasa harkar noma, a wani mataki na kokarin rage dogaro da man fetir da kuma shigo da kayayyakin abinci daga kasashen waje. Sai dai wasu manoman timatir sun koka kan rashin tallafi daga gwamnati.
Sauran kashi-kashi
-
Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da ta'azzara a Najeriya
Shirin zai maida hankali ne kan hahoton baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Najeriya ta fitar wanda ya bayyana yadda kasar ke ci gaba da fuskantar karin hauhawar farashin kayayyaki musamman na abinci, mafi muni da kasar ta gani a sama da shekaru 20. Rahoton wanda National Bureau of Statistic ta fitar a makon da ya gabata, ya cewa an fuskacin hauhawan farashin kayayyaki da sama da kashi 33 da rabi cikin 100 a watan Afrilun da ya gabata.22/05/202410:43 -
CAC a Najeriya ta bai wa masu sana'ar POS wa'adin watanni biyu su yi ragista
Shirin 'Kasuwa akai Miki Dole na wannan makon tare da Ahmad Abba ya maida hankali ne kan matakin gwamnatin Najeriya bukatar masu sana'ar POS da sauran masu mu'amala da na'urar da su garzawa hukumar rajistan kamfanoni ta kasar domin yin ragista kafin ranar 7 ga watan Yulin wannan shekara ta 2024.15/05/202411:24 -
Yadda matsin rayuwa ya tilastawa 'yan Najeriya fasa rumbunan abinci
Shirin Kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yada zango ne a Tarayyar Najeriya, inda ya yi dubi kan matsanancin kuncin rayuwar da al’umman kasar suka shiga da har ta kai ana fasa rumbunan abinci ko tare manyan motocin dakon kaya a tituna ana kwasan abinci.06/03/202410:22 -
Faduwar darajar Naira ta tsayar da harkokin 'yan canji a makwaftan Najeriya
Shirin 'Kasuwa a kai miki dole' na wannan mako ya tattauna akan yadda faduwar darajar Naira ke haddasa koma bayan kasuwar 'yan canji a makwaftan Najeriya.07/02/202410:19 -
Dalilan soke lasisin wasu kamfanonin wutar lantarki
Shirin Kasuwa a Kai Maki Dole na wannan mako, ya mayar da hankali ne a game da batun wutar lantarki a Najeriya, bangaren da ke fama da matsalololi tsawon shekaru.Shirin zai yi dubi ne a game da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sokewa da kuma sabunta lasisi ga wasu kamfanonin da ke da alhaki rarraba wuta a cikin kasar.31/01/202410:02