Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

An dakile harin Boko Haram a kauyen Abadam da ke Borno

Bataliyar Sojojin Najeriya dake kauyen Abadam na Jihar Borno ta dakile harin da mayakan Boko Haram suka kaiwa barikinsu a jiya Alhamis.

Sojojin Najeriya da ke cikin rundunar "Operetion Lafiya Dole"
Sojojin Najeriya da ke cikin rundunar "Operetion Lafiya Dole" AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Wata majiya mai tushe ta ce yayin gwabza fadan, sojin Najeriya sun samu nasarar kashe mayakan Boko Haram 15, yayin da wasu da dama daga cikinsu suka tsere da raunuka.

Majiyar ta kara da cewa, Sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin kokarin dakile harin na kungiyar ta Boko Haram.

Sojojin Najeriyar sun samu nasarar kwato tarin makamai da suka hada da bindigogi da alburusai daga mayakan, sai kuma wata bindiga da ake amfani da ita wajen kakkabo jiragen sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.