Isa ga babban shafi
Najeriya

Sanatocin Najeriya sun bijire wa Saraki

Mambobin majalisar dattawan Najeriya sun ki amincewa da shugabansu Sanata Bukola Saraki bayan ya bukaci gwamnatin kasar ta siyar da wasu kadarorin da ta mallaka. 

Mambobin majalisar dattawan Najeriya
Mambobin majalisar dattawan Najeriya
Talla

Mr. Saraki ya shiga sahun wasu tsirarun mutane da ke bukatar a siyar da kadarorin don samun kudaden farfado da tattalin arzikin kasar da ke cikin mawuyacin hali.

Akasarin ‘yan majalisar da suka tofa albarkacin bakinsu a muhawarar da aka tafka kan koma-bayan tattalin arzikin, sun zargi wasu mutane kalilan da hannu wajen haifar da matsalar ta tattalin arziki a kasar.

Sai dai Sanatocin sun bukaci gwamnati ta sake nazari kan tsarinta na asusun bai daya, abin da suka bayyana a matsayin daya daga cikin matsalolin da suka haifar da karanci kudi a hannun jama’a.

Dangane da takaddama kan siyar da kamfanonin gwamnatin Najeriya, Gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar ya yi mana tsoakaci

01:00

BADARU ABUBAKAR KAN TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.