Isa ga babban shafi
Najeriya

An kashe 'yan sandan Najeriya a bakin aiki

Rahotanni daga Jihar Benue da ke Najeriya sun ce ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 4 a wani harin da suka kai ofishinsu da ke Igumale a karamar hukumar Ado ta jihar.

Wasu daga cikin jami'an tsaron Najeriya
Wasu daga cikin jami'an tsaron Najeriya Reuters/Akintunde Akinleye
Talla

Daya daga cikin jagororin al'ummar yankin, Ajibo Ochulayi ya bayyana cewa, maharan sun yi nasarar awon-gaba da bindigogin jami’an tsaron bayan sun hallaka su a cikin daren jiya.

Mr. Ochulayi ya ce, nan take 'yan sanda biyu suka riga mu gidan gaskiya yayin da sauran suka mutu a wata cibiyar kula da marasa lafiya ta birnin Makurdi.

Tuni dai kwamishinan 'yan sandan jihar, Bashir Makama ya ziyarci in da lamarin ya auku tare da rakiyar jami'an tsaro.

Jihar ta Benue na yawan fama da hare-hare a cikin 'yan watannin nan sakamon rikici tsakanin manoma da makiyaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.