Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Sanata Wakili kan dokar daidato a Najeriya

Wallafawa ranar:

A Najeriya, yanzu haka dai jama’a sun zura wa Majalisar dattawan kasar ido domin ganin irin matakin da za ta dauka a game da wani daftarin doka da ke neman samar da daidaito tsakanin maza da mata hatta ta fannin rabon gado da dai sauransu.Tuni dai shugabannin addinai suka gargadi ‘yan majalisar da kada su amince da wannan daftari na doka, bayan da aka samu labarin cewa tuni daftarin ya tsallake zuwa mataki na gaba. To sai dai a zantawarsa da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, Sanata Ali Wakili, ya ce majalisar dattawan ba za ta amince da wannan doka ba.

Majalisar dattawan Najeriya
Majalisar dattawan Najeriya
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.