Isa ga babban shafi
Najeriya-Tattalin Arziki

Gwamnatin Najeriya na shirin ganawa da shugabannin Niger Delta

Gwamnatin Najeriya na shirin ganawa da shugabanin kabilun Naija Delta da kuma tsagerun dake fasa bututun mai a makon gobe, domin ganin an kawo karshen tashin hankalin da ake samu a Yankin.

Tsagerun yankin Niger Delta suna barna a Najeriya
Tsagerun yankin Niger Delta suna barna a Najeriya
Talla

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya ruwaito majiyar gwamnatin kasar na cewa za’a gudanar da taron ne ranar litinin mai zuwa a Abuja.

Ana saran shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Ministan mai Ibe Kachikwu su jagoranci taron.

Gwamnatin Najeriya ta shafe watanni tana kokarin kawo karshen tashin hankalin da ke aukuwa a yankin Niger Delta, sai dai har yanzu bata samu nasarar cimma hakan ba.

Tsagerun Niger Delta Avengers, wadanda tun a farkon shekara ta 2016 suke daukar alhakin fasa tarin bututun mai, sun bayyana dakatar da kai hari a watan Agusta, sai dai kuma a watan Satumban da ya gabata suka kara kai wani harin na lalata butun mai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.