Boko Haram ta yi wa sojin Najeriya kwanton-bauna
Akalla sojojin Najeriya da jami’an kato da gora tara ne suka rasa rayukansu sakamakon kwantar-baunar da mayakan Boko Haram suka yi musu a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno ta tarayyar Najeriya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sojoji 19 ne suka jikkata a sanadiyar farmakin wanda aka kai musu a dai dai lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa sansaninsu bayan samamen da suka kai wa Boko Haram a kauyan Ugundiri da ke karamar hukumar Damboa.
Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Kanar Sani Usman ya tabbatar da aukuwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, in da ya ce, tuni aka garzaya da sojojin da suka riga mu gidan gaskiya zuwa birnin Maiduguri, yayin da kuma jami’an da suka samu rauni ke samun kulawa a asibitin soji.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu