Najeriya
Tsagerun Neja Delta sun fasa bututun tura mai zuwa Turai
Kungiyar Tsagerun Najeriya da ake kira Neja Delta Avengers sun dauki alhakin kai hari tashar fitar da danyan man fetur din kasar zuwa kasuwannin duniya mallakar kamfanin Shell.
Wallafawa ranar:
Talla
Mai Magana da yawun kungiyar, ya sanar ta kafar sadarwar twitter cewar, su suka fasa bututun man.
Rahotanni sun tabbatar da fasa bututun ranar talata, wanda ake ganin babbar koma baya ne ga yunkurin gwamnatin kasar na sasantawa da mutanen Yankin Neja Delta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu