Najeriya zata samar da abinci mai gina jiki ga akalla yara miliyan 2
Majalisar Dattawan Najeriya ta ce zata amince da samar da kudi naira biliyan 95 cikin shekara ta 2017 don samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara miliyan daya da dubu dari tara, dake fama da rashin abincin mai gina jiki.
Wallafawa ranar:
Shugaban kwamitin Majalisar kan fannin lafiya Sanata Olanrewaju Tejuoso ya sanar da hakan, yayin da yake tabbatar da cewa a ba’a baiwa fannin samar da abinci mai gina jiki muhimmanci ba a kasafin kudi na 2016.
A bangare guda kuma asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce zai bada taimakon tallafawa yara 600,000 wajen magance musu rashin abinci mai gina jiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu