Yau Majalisar Najeriya ke tantance Ibrahim Magu
Yau ne Majalisar Dattawan Najeriya ke gudanar da zama na musamman don tantance shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Ibrahim Magu, kamar yadda mataimakin kakakin Majalisar, Ike Ekweremadu ya sanar.
Wallafawa ranar:
Wannan na zuwa ne bayan watanni biyar da fadar shugaban kasa ta gabatar da Magu ga Majalisar don amincewa da shi a matsayin shugaban hukumar ta EFCC.
Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Magu a matsayin mukaddashin hukumar EFCC bayan sauke Ibrahim Lamorde a ranar 9 ga watan Nuwamban bara.
Matukar dai aka tabbatar da shi a yau, Magu zai kasasne mutun na hudu da ya shugabanci hukumar bayan Nuhu Ribadu da Farida Waziri da kuma Ibrahim Lamorde
Masu sa ido na kallon matakin tabbatar da shi a matsayin abin da zai ba shi karfin gwiwar ci gaba da dirar mikiya kan barayin dukiyar talakawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu