Isa ga babban shafi
Najriya

Najeriya ta fitar da sabbin sharuddan aikin hajji

Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya ta fitar da wasu sabbin sharudda da ta ce dole ne, duk wani maniyyaci ya cika su kafin ba shi damar zuwa aikin hajji a Saudiya. 

Wasu daga cikin Alhazan da suka yi aikin hajji a can baya
Wasu daga cikin Alhazan da suka yi aikin hajji a can baya AFP
Talla

A cewar shugaban sashin hulda da kafafen yada labaran hukumar, Alhaji Uba Mana, sharudan za su taimaka wajen kawo karshen samun masu safarar miyagun kwayoyi da ke shiga cikin maniyatan Najeriya, da kuma aikata sauran laifuka a yayin aikin hajji.

Mana ya ce yanzu tilasne  maniyyaci ya gabatar da wani sahihin mutum, da zai tsaya masa kafin ba shi damar zuwa aikin hajji, wadanda suka hada da, limamin masallacin Juma’a da ma’aikacin gwamnati da ke mataki na 12, ko kuma mai mukamin sarautar gargajiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.