Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano ma'aikatan boge dubu 50 a Najeriya

Fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce, a cikin wannan shekara da ke karewa, ta gano ma’aikatan boge akalla dubu 50 a fadin kasar, kuma hakan ya bayar da damar tsimin kudaden da yawansu ya kai Naira milyan dubu 200.

shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Mai magana da yawun shugaban kasar Garba Shehu ya ce, an cafke mutane 11 da ke tafiyar da wannan yaudara ta ma’aikatan boge tare da mika su ga hukumar yaki da rashawa ta kasar, EFCC.

Shehu ya ce, kafin gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin bincike a cikin watan Fabairun da ya wuce domin tantance adadin ma’aikata na gaskiya, ana biyan albashin Naira milyan dubu 151 a kowane wata, to amma bayan gano ma’aikatan na boge albashin ya dawo zuwa Naira milyan dubu 138, abin da ke nufin cewa, gwamnatin na tsimin Naira biliyan 13 a kowane wata a yanzu.

Tuni dai gwmnatin Buhari ta kudiri aniyar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.