Isa ga babban shafi
Najeriya

Gobara ta kona shaguna fiye da 50 a Potiskum

Wata gobara da ta tashi a kasuwar garin Potiskum da ke jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta kona akalla shaguna 50 na jama’a. 

Gobara ta kona shaguna jama'a fiye da 50 a kasuwar Potiskum da ke jihar Yobe a Najeriya
Gobara ta kona shaguna jama'a fiye da 50 a kasuwar Potiskum da ke jihar Yobe a Najeriya
Talla

Gobarar wadda ta shi da misalin karfe 1 na daren daya gabata, ta fi yin illa a bangaren masu hada-hadar kayan gwanjo da teloli da kuma bangaren da ake siyar da kwanuka.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Isa Sakatare ya shaida wa RFI hausa cewa, sun kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike don kiyasta girmar dukiyar da aka yi asarar ta a gobarar.

Shugaban dai ya tabbatar cewa, gobarar ta haifar da gagarumar asarar da ba zai iya kiyasta ta ba har sai kwamitin ya fitar da sakamakon bincikensa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.