Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na shirin magance karancin lantarki

A Najeriya sakamakon matsalar wutar lantarki da ake fama da ita, gwamnatin tarayya ta ba da kwangilar fadada wata cibiyar samar da wutar lantarki da ke Odogunyon a Ikorodu na jihar Legas. 

Ana fama da karancin wutar lantarki a sassan Najeriya
Ana fama da karancin wutar lantarki a sassan Najeriya REUTERS/Vasily Fedosenko
Talla

An ware kudade Naira miliyan dubu uku da dari biyar domin wannan aiki, kamar dai yadda taron majalisar koli ta kasar da aka gudanar a wannan laraba ya sanar.

Ministan manyan ayyuka, gine-gine da kuma makamashi, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa, wannan kwangilar za ta bada damar samar da tiransifomomi da kuma layukan jan wuta, abin da zai taimaka wajen samun wutar lantarki akai akai a yankin.

Fashola ya ce, tun a cikin shekarar 2009 ne aka bada kwangilar fadada cibiyar amma aka yi watsi da ita saboda karancin kudi.

Jama'a da dama a sassan Najeriya na fama da karancin wutar lantarki, lamarin da ke haifar da cikas ga harkokin kasuwancin wasu daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.