Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Harin Boko Haram ya hallaka sojoji 3

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla sojojin kasar 3 ne suka mutu lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari wajen wani binciken ababan hawa na sojojin a kauyen Kamuya da ke kusa da garin Buratai.

Boko Haram ta kai harin na yau a kauyen Kamuya da ke kusa da garin Buratai.
Boko Haram ta kai harin na yau a kauyen Kamuya da ke kusa da garin Buratai. AFP PHOTO/STRINGER
Talla

Daya daga cikin sojojin da ke wurin ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar maharan sun isa kauyen ne akan rakuma, inda suka bude musu wuta.

Daga bisani mayakan sun sanar da kashe sojoji 5 da kuma jikkata wasu 11, amma rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai kan harin ba tukuna.

Rundunar Sojin Najeriya na ci gaba da kokarin kakkabe sauran mayakan kungiyar Boko Haram da suka yi saura a yankin arewa maso gabashin kasar sai dai suna fuskantar tirjiya daga mayakan kungiyar da ke kai hare-hare lokaci zuwa lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.