Jami'an 'yan sanda sun shirya dakile zanga zanga a Najeriya
Rundunar ‘Yan sanda a birnin Legas ta dauki matakan rarraba jami’anta zuwa sassa daban daban na titunan birnin, don dakile duk wani yunkuri na gudanar da zanga zangar da mawaki Tuface Idibia ya shirya jagoranta.
Wallafawa ranar:
A dai ranar lahadin da ta gabata mawakin ya sanar da cewa ya janye kudurinsa, saboda kaucewa tada zaune tsaye.
A satin da ya gabata Tuface ya bukaci da a fito zanga zangar nuna rashin jin dadin koma bayan tattalin arziki da Najeriya ke fuskanta.
Rahotanni sun ce sama da ‘yan sanda 100 aka girke tu misalign karfe 7 agogon Najeriya, a filin wasanni na Surulere da ke birnin Legas da ke kudancin Najeriya.
Zalika Kwamishinan ‘yan sandan jihar Fatai Owoseni ya kasance a filin wasan na Surulere, tare da rakiyar motoci ‘yan sanda 15 da motar sulke guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu