Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya zata karbo bashin dala biliyan $2.3

Ministan kudin Najeriya Kemi Adeosun ta ce kasar zata karbo bashin dala biliyan 1 daga bankin duniya, nan da watanni kadan kuma, zata sanya hannu kan yarjejeniyar karbar bashin dala biliyan 1 da miliyan 3 daga kasar China.

Ministan kudin Najeriya Kemi Adeosun
Ministan kudin Najeriya Kemi Adeosun newsflash
Talla

Adeosun ta ce za’a yi amfani da kudaden wajen karasa shimfida layukan dogo da zai sada sassan kasar, da kuma cike gibin kasafin kudin kasar na bana na naira triliyan 7.3.

Kimanin shekara guda kenan, gwamnatin Najeriya tana tattaunawa da bankin duniyar kan karbar bashin, wadda ake sa ran karkarewa cikin wannan watan.

Zalika tuni bankin Export-Import na kasar China ya amince da bawa Najeriyar bashin na dala biliyan 1 da miliyan 300.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.