Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Adamawa ta daure tsohon gwamnan jihar Bala Ngilari

Wata kotu a Adamawa dake Najeriya ta yankewa tsohon Gwamnan Jihar, Bala James Ngilari hukuncin daurin shekaru 5 a gidan yari saboda samun sa da laifin karya dokar bayar da kwangila.

Tsohon gwamnan jihar Adamawa Bala James Ngilari.
Tsohon gwamnan jihar Adamawa Bala James Ngilari. dailypost.ng
Talla

Alkalin kotun Nathan Musa, yace ya gamsu da shaidun da aka gabatar masa dangane da zargin da ake yiwa tsohon gwamnan, inda ya bada umurnin daure shi na shekaru biyar ba tare da zabin biyan tara ba.

Sai dai alkalin kotun ya bai wa Ngillari zabin gidan yarin da yake so a aiwatar masa da hukuncin.

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya EFCC ce tagurfanar da tsohon gwamnan tare da Sakataren gwamnatinsa Ibrahim Weyle, sai kuma kwamishinan kudinsa Sanda Lamurde, bisa laifin sabawa dokokin bada kwangilar sayan motoci kirar Hilux kan kudi naira miliyan 167.8 a lokacin da suke bakin aiki.

To sai dai kuma kotun ta wanke sauran mutane biyun, yayinda ta yankewa tsohon gwamna, bala Ngilari hukuncin na shekaru 5 a gidan yari.

Ngilari ya kasance mataimakin gwamna ga yayin mulkin tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako tsawon shekaru 7, har zuwa lokacin da aka tsige Nyako a watan July na shekara ta 2014.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.