Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun yi karin haske kan kama Sule Lamido

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar kano ta kama tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, saboda zargin tinzira magoya bayan sa su hana zaben kananan hukumomi a Jihar.

‘Yan Sandan Jihar kano ta kama tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido
‘Yan Sandan Jihar kano ta kama tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido premiumtimesng.com
Talla

Wakilinmu da ke Kano Abubakar Dandago ya tabbatar mana da cewar an kama tsohon Gwamnan kuma yanzu haka yana Cibiyar ‘Yan Sanda shiya ta daya inda suke gudanar da bincike.

Kakakin Rundunar da ke birnin Kano DSP Sambo Sokoto, ya ce kamun ya biyo bayan wasu korafe-korafe ne da gwamnatin jihar ta Jigawa ta shigar a game da wasu kalaman da tsohon gwamnan ya furta.

Lamido wanda aka kama a gidansa da ke Sharada tun safiyar ranar Lahadi, rundunar ta ce ba za ta iya tabbatar da hakikanin lokacin da za a sake shi ba.

Tsohon gwamnan na daya daga cikin jiga-jigan 'ya'yan babbar jam'iyyar adawa ta PDP, a Najeriya, kuma ya sha sukar irin kamun ludayin gwamnatin kasar ta jam'iyyar APC.

Gwamnatin Jihar Jigawa dai ta sanya ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa a matsayin ranar gudanar da zaben kananan hukumomi a Jihar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.