Isa ga babban shafi
Najeriya

Masu kishin al'umma sun bukaci a yi hattara a Kano

Gamayyar kungiyoyin kishin al'umma a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun bukaci gwamnatin jihar da kuma masaurtar Kano da su yi hattara da wani rukunin mutune da ke kokarin amfani da sabaninsu wajen ruruta wutar rikici a fadin jihar.

Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta binciki masarautar jihar bisa zargin ta da barnatar da dukiya ba bisa ka'ida ba
Hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano ta binciki masarautar jihar bisa zargin ta da barnatar da dukiya ba bisa ka'ida ba REUTERS/Joe Penney
Talla

Gamayyar kungiyoyin sun kuma ja hankulan bangarorin biyu kan mummunan sakamakon da al'ummar jihar za su fuskanta sanadiyyar rikicin wanda wasu ke aiki ta karkashin kasa domin ganin cewar ba a kai ga warware sabanin ba.

Kungiyar ta ce za ta ci gaba da aiki tare da dukkanin masu ruwa da tsaki a lamarin domin ganin sulhu tsakin bangarorin biyu ya dore don kawar da barazanar tsaro.

Ga abin da Kakakin gamayyar Kungiyoyin Kwamared Abdulmajid Sa'ad ya  shaida wa RFI hausa.

00:50

Kwamared AbdulMajid Sa'ad kan rikicin Kano

Ana ganin binciken da hukumar sauraren korafin jama'a da kuma yaki da cin hanci ta Kano ta yi Masarautar jihar bisa zargin barnatar da makuden kudade ba bisa ka'ida ba, wani abu ne da ya fito da sabani tsakanin gwamnatin jihar da kuma Masarautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.