Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Mayakan Boko Haram sun yi wa ayarin motoci kwanton bauna

A jihar Borno da ke Najeriya, bayanai na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton cewa ‘yan Boko Haram ne, sun kai harin kwanton bauna a kan ayarin motocin da ke hanyar Maiduguri zuwa Damboa a jiya Talata, duk da cewa ayarin na tare da rakiyar sojoji kamar yadda aka saba.

Mayakan kungiyar Boko Haram
Mayakan kungiyar Boko Haram pmnewsnigeria
Talla

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Borno Damien Chukwu ya tabbatar da mutuwar dan sanda daya da kuma direban wata mota.

Sai dai shaidu sun ce adadin zai iya zarta haka, idan aka yi la’akari da cewa akwai wasu jami’an ‘yan sanda akalla 63 daga cikin ayarin, bayan an canza ma su wurin aiki, sannan kuma suke dauke da wata gawa da ya kamata su kai a can garin na Damboa.

Akalla motoci 200 ne ke cikin ayarin da ke tafiya, inda wata Bus mai dauke mutane 80 ke dauke da ‘yan sandan da aka yiwa canjin aiki daga Oghara a jihar Delta zuwa Askira Uba, daya daga cikin yankunan da aka yanto daga hannun mayakan Boko Haram.

Wani da shaida lamarin, ya bayyana wa RFI hausa cewa, an dauki lokaci ana musayar wuta tsakanin mayakan da Jami’an tsaron, daga bisani kuma jiragen yaki suka kawo dauki.

01:26

Mayakan Boko Haram sun yi wa ayari kwanton bauna

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.