Isa ga babban shafi
Najeriya

Mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 18 a Banki

Rahotanni daga garin Banki da ke kudu maso gabashin jihar Borno, a kan iyakar Najeriya da Kamaru, na cewa wasu mayakan Boko Haram sun hallaka mutane 18 a daren jiya Juma’a.

Wasu sojin kasar Kamaru yayin da suke sintiri a garin Amchide a arewacin Kamaru, da ke da nisan kilomita 1 daga kan iyakar Najeriya.
Wasu sojin kasar Kamaru yayin da suke sintiri a garin Amchide a arewacin Kamaru, da ke da nisan kilomita 1 daga kan iyakar Najeriya. AFP
Talla

Daya daga cikin ‘yan kungiyar sa kai ta Civilian JTF, Modu Perobe, ya ce mayakan sun yi amfani ne da takubba da wukake wajen afkawa wasu mazauna garin na Banki cikin dare.

A ‘yan watannin baya-bayannan dai ana fuskantar karuwar hare-haren mayakan na Boko Haram a Jihar Borno, inda zuwa yanzu akalumma suka nuna cewa daga ranar 1 ga watan Yuni, zuwa Alhamis din data gabata, akalla mutane 172 ne suka rasa rayukansu, sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya rawaito.

Sabon harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da Sakataren hakokin wajen Birtaniya Boris Johnson, yace yanzu haka kasarsa na horar da sojojin Najeriya dubu 28,000 domin tinkarar mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, in da matsalar ta fi kamari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.