Isa ga babban shafi
Najeriya

An hana fitar dare a Abia da ke Najeriya

Gwamnatin Jihar Abia da ke yankin kudancin Najeriya ta kafa dokar hana fitar dare har tsawon kwanaki uku sakamakon arangamar da aka yi tsakanin masu fafutukar kafa kasar Biafra da sojojin gwamnati.

Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra
Wasu 'yan kungiyar IPOB masu ra'ayin kafa kasar Biafra http://naijagists.com
Talla

Dokar wadda ta fara aiki tun a ranar Talata, ta takaita zirga-zirgar mutane daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, kuma za ta ci gaba da aiki har zuwa ranar jumma’a.

Gwamnan jihar Okezie Ikpeazu ya ce, za su ci gaba da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya kuma jiharsa za ta yi aiki da gwamnatin tarayya wajen murkushe barazanar masu neman raba kasar.

Gwamnan ya bukaci sojin kasar da su gudanar da ayyukansu a jihar cikin tsanaki tare da mutunta hakkin dan adam.

Arangamar na zuwa ne a yayin da sojojin Najeriya suka kaddamar da wata  runduna ta musamman mai suna Operation Python Dance II, wadda za ta sanya ido kan matsalar garkuwa da mutane da fashi da makami da kasashe-kashe da kuma ayyukan masu fafutukar raba kan kasar a yankin kudu maso gabashin Najeriya.

A bangare guda rahotanni daga Umuahia sun ce akalla hausawa 3 aka kashe a harin da aka kai musu bayan arangamar da sojojin suka yi da masu fafutukar kafa kasar ta Biafra.

Wani mazaunin garin ya shaida wa sashen na RFI cewa, kimanin hausawa dubu 2 sun nemi mafaka a masallaci, yayin da aka jibge jami’an tsaro don tabbatar da lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.