Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya koka kan cinkoson mutane a gidajen yari

Shugaban Najeriya Muhd Buhari ya koka kan halin da gidajen yarin kasar ke ciki, lamarin da ya bayyana a matsayin wata matsala ga kimar kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

A cewar shugaban, da dama daga cikin gidajen yarin na fama da cinkoson mutane da kashi 90 cikin 100.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da ya gana da tawagar alkalan kasar karkashin jagorancin Mai Shari’a, Walter Onnoghen a fadarsa da ke birnin Abuja a jiya Jumma’a.

Shugaba Buhari ya ce, akwai bukatar samar da sabbin matakan gaggawa don rage cinkoso a gidajen yarin da ke sassan Najeriya.

Shugaban na ganin cewa, daukan matakin na da muhimmaci wajen rage kudaden kula da gidajen yarin da kuma inganta lafiyar mutanen da ke kulle a cikin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.