Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bullar Karanbon Birai
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da samun cutar da ake kamuwa da ita, a dalilin cin naman biri, da ake kira monkeypox, bayan gwajin da akayi sakamakon samun alamun cutar a jihohi 7.
Wallafawa ranar:
Ministan lafiya na kasar Isaac Adewole yace an samu samfurin cutar 17 a Jihar Bayelsa, kuma gwajin da akayi a cibiyar Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dake Senegal ya tababtar ad cewar cutar ce.
A nata bangaren, ma’aikatar lafiya ta Najeriyar tace mutane 43 ne suka nuna alamun kamuwa da cutar a Jihohi 6 dake Yankin kudancin kasar da suka hada da Legas, sai kuma Abuja daga Arewa.
Yayin zantawarsa da sashin Hausa na RFI, Dr Muhammed Aliyu, na Cibiyar yaki da cututtukan dabbobi dake Vom a Najeriya, yayi mana bayani akan yadda za’a kaucewa kamuwa da cutar.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da bullar Kyandar Birai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu