Isa ga babban shafi
Nigeria

Ana babban taron PDP a Abuja

Dubban magoya bayan babban jam'iyyar adawa a Najeriya PDP ne suka taru a dandalin Eagle Square da ke birnin Abuja domin gudanar da babban taronta na kasa.

Tsohon shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP Goodluck Jonathan. REUTERS/Stringer
Talla

A lokacin wannan taro ne ake sa ran 'ya'yan jam'iyyar za su zabi sabon shugabanta na kasa, wanda zai maye gurbin shugaban riko na jam'iyyar Ahmed Muhammad Makarfi.

Rahotanni daga birnin na Abuja sun ce an jibge jami'an tsaro a wurare na musamman kusa da dandalin taron domin tabbatar da tsaro.

Wannan ne karo na farko da jam'iyyar za ta gudanar da babban taro bayan dogon lokacin da aka kwashe ana shari'a a game da shugabancin jam'iyyar tsakanin Sanata Ali Modu Sherif da Ahmed Makarfi.

Jiga-jigan jam'iyyar daga fadin kasar sun hallara a wurin taron, daga cikin su har da tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar APC mai mulkin kasar zuwa PDP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.